Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, wani limamin Abuja, Fasto Prize Aluko, ya roki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya tsaya takara a karkashin jam’iyya mai mulki..
Babban limamin cocin The Resurrected Assembly (GROM), kuma mai gabatar da addu’o’in ministocin Abuja (AMPO), ya bayyana cewa duk abin da ke faruwa a yau a siyasar tsohon shugaban kasa, cikar annabcin Allah ne tun 2020.
Ya kara da cewa, bisa ga ikon Allah, ko wanene ya fito takarar shugaban kasa daga wasu jam’iyyun siyasa, jam’iyyar APC za ta ci gaba da samun nasara a 2023 tare da Jonathan a matsayin dan takararta na shugaban kasa.