‘Yan sandan Jihar Ogun sun kama wani malamain majami’a, Peter Omope, kan yunkurin kisa da mallakar makami da aka haramta.
A rahoton the Punch, ta ce, an kama faston mai kula da cocin Celestial Church of Christ, yankin Yesu Yan, da ke Olambe Junction, Akute Jihar Ogun, kan harbin wata bakuwar mai ibada, Kemi Johnson, a kofar shiga cocin.
Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Oyeyemi ya ce, an kama wanda ake zargin ne bayan wani Olalekan ya kira ofishin ‘yan sanda an yi korafi.
Oyeyemi ya kuma ce, Olalekan ya shaidawa ‘yan sandan cewa, shi da Kemi Johnson ‘yar shekara 18 sun kai matar da suke yi wa aiki ne filin tashin jiragen sama ne.