fidelitybank

Makwabtan Najeriya ne ke janyo ake kashe makuden kudade – Gwamnati

Date:

Ministan kudi da tattalin arziki na kasa, Wale Edun, ya ce, a na kashe dimbin kudin da ya kai dala miliyan 600, kwakwankwacin sama da naira biliyan 956.370 a duk wata wajen siyo mai daga waje, saboda makwabtan kasashe na cin moriyar man na Najeriya.

Ministan ya ce kasashen da ke amfani da man da Najeriyar ke siyowa daga waje ba wai makwabtanta ba ne na kusa har ma zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato Santa Afirka.

Ya ce, ”ba Najeriya kadai muke sayo wa ba, muna saya wa kasashe ta gabas, har zuwa Afirka ta Tsakiya. Muna saya wa kasashe na arewa, muna saya wa kasashe na yamma.

Saboda haka dole ne mu tsaya mu tambayi kanmu, har zuwa yaushe za mu ci gaba da yin haka, to wannan shi ne muhimmin abu da ya shafi tattalin arzikinmu.”

Mista Edun wanda ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na AIT, ya kara da cewa wannan shi ne ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin mai, saboda Najeriya ba ta san ainahin adadin man da take amfani da shi ba a cikin gida.

Ministan ya ce wannan shi ya sa dole Najeriya ta dauki tsattsauran mtaki kan matsalar saboda tana hana bunkasar tattalin arzikin kasar.

Hukumar kididdiga ta kasar ta ce, yawan man da kasar ke shigowa da shi daga waje ya ragu zuwa kusan lita biliyan daya a wata bayan da Tinubu ya cire tallafin man, ranar 29 ga watan Mayu na bara.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp