Abdullahi Nyako, sakataren sirri na dan takarar shugaban kasa a jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar, ya rasu.
Mai taimaka wa Atiku kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa.
Ya ce Nyako, wanda lauya ne, ya mutu da sanyin safiyar Alhamis.
Ibe bai bayyana musabbabin mutuwar ba, amma ya bayyana Nyako a matsayin âdadewar abokin tarayya kuma mai kula da tsohon mataimakin shugaban kasaâ.
âAbdullahi ya fi mataimaki, dangi ne a gare ni ta kowace fuska. Ya bauta mini da aminci da himma. Za a yi kewarsa sosai.
âA madadin iyalina, ina so in mika sakon taâaziyyata ga iyalan Nyako tare da yi musu adduâar Allah Madaukakin Sarki Ya yi musu taâaziyya da karfafa musu gwiwa. Allah ya gafarta masa, ya saka masa da Aljannar Firdausi. Ameen,â sanarwar ta kara da cewa.
Mutuwar Nyako ta zo ne shekaru uku bayan Atiku ya rasa wani na kusa da shi Umar Pariya.