Tsohon ministan yada labarai kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Labaran Maku ya janye aniyarsa na tsayawa takarar gwamna sa’o’i bayan fara kada kuri’a.
Maku ya bayyana haka ne a ranar Laraba a wurin da za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a karamar hukumar Nasarawa Toto bayan wata ‘yar gajeriyar ganawa da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Da yake mayar da martani kan janyewar tasa, Maku ya ce bayan tattaunawa da abokansa da abokan huldarsa ya yanke shawarar janye aniyarsa ta tsayawa takara a zaben fidda gwani.
Da aka tambaye shi ra’ayinsa kan yadda zaben fidda gwanin da ke gudana tsohon ministan ya ce ‘Babu Magana.
Idan dai za a iya tunawa, Daily Sun ta ruwaito cewa dukkan ‘yan takarar guda uku, David Ombugadu, Nuhu Amgbazu da Labaran Maku, sun amince su yi aiki tare domin kayar da wanda ke kan karagar mulki.