fidelitybank

Mako mai zuwa za a dakatar da karbar harajin shigo da kayan abinci – Kwastan

Date:

Gwamnatin Tarayya ta ce, daga mako mai zuwa ne za a fara aiwatar da umarnin da ta bayar na dakatar da karbar haraji a kan kayayyakin abinci da ake shigar da su kasar daga waje.

Tun a watan Yuli ne gwamnatin ta sanar da cewa ta amince da wa’adin kwana 150 na shigar da masara da shinkafa da alkama daga waje ba tare da biyan haraji ba, domin magance matsalar tsadar kayan abinci a kasar, to amma har yanzu ba a ga hakan ba, inda ‘yan kasuwa ke korafi da cewa ba su gani a kasa ba.

To amma da yake jawabi a lokacin taron shugabannin hukumomin tsaro na kasar da aka yi jiya Talata a Abuja, shugaban hukumar hana fasa kwauri, Bashir Adeniyi, ya ce za a fara aiwatar da shirin da zarar an kammala tsara ka’idojin da aka shimfida.

Ya ce: “Ana fayyace ka’idojin a ma’aikatar kudi, kuma ina tabbatar muku cewa zuwa mako mai zuwa, za a kammala fitar da ka’idojin…”

Ya ce an samu jinkirin aiwatar da tsarin ne domin ganin an yi laka’ari da yadda zai amfani dukkanin masu ruwa da tsaki da suka hada da manoma.

Shugaban na kwastan ya ce tuni ma wasu daga cikin kayan abin sun riga sun shigo kasar, kuma za a fitar da su ba tare da biyan haraji ko kudin fito ba.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp