Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce kada wani ya kuskura da yin tunanin cewa za su samu nasara a kasar a daidai lokacin da masu zanga-zangar adawa da gwamnati ke shiga mako na biyar.
Ali Khamenei ya ce Iran ba za ta girgiza ba kuma babu wanda ya isa ya rusa kasar ta musulunci.
Shi ma shugaban kasar, Ebraim Raisi, ya zargi makiya da kokarin kawo tarnaki a kasar.
Ya godewa al’ummar Iran saboda goyon bayan gwamnati da suke yi musamman ma a wannan lokaci da kasar ke kokarin farfado da tattalin arzikinta, inda ya ce kasar na samun ci gaba cikin sauri.