Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci taron kaddamar da kwamiti na yakin neman zaben gwamnan jihar Osun.
A wata hira da jaridar The Punch, mai magana da yawun gwamnan, Taiwo Adisa, ya bayyana cewa, gwamnan ba zai iya halartar taron ba saboda zai bar kasar.
Ya bayyana cewa Gwamna Makinde ya je Isra’ila ne domin halartar taron zuba jari.
“Gwamnan baya kasar ne don halartar wani taron zuba jari na Agribusiness a Isra’ila,” in ji shi.
Har ila yau, mai baiwa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto shawara kan manufofin ci gaba mai dorewa, Kabiru Aliyu, ya bayyana cewa, gwamnan ya je kasar Jamus ne domin wani muhimmin taro.
Sai ya yi zargin cewa, Tambuwal bai halarci taron ba ne saboda wasu rashin jituwa a jam’iyyar.
Wani karin rahoto ya nuna cewa Waziri ya gana da Wike a kasar Turkiyya inda ya roke shi da ya goyi bayan aniyar Atiku ta zama shugaban kasa, lamarin da ya yi watsi da shi.
Wike dai ya yi shiru kan tafiyar da jam’iyyar bayan da Atiku ya yi watsi da shi wanda ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.
Ibe ya mayar da martani da cewa, za a warware matsalolin da Wike da sauran shugabannin da suka ji haushi.