Shahararren mawaƙin fina-finan Bollywood a kasar Indiya, Bappi Lahiri, wanda aka sani da waƙoƙin disko da kuma caɓa kwalliya, ya mutu ya na da shekara 69 a duniya.
Lahiri wanda ya warke daga cutar korona a watan Afrilun da ya wuce, ya shafe watan da ya gabata a asibiti, sai mutu a jiya Talata.
Salon kiɗansa na disko ya sa masu kallo sun shaƙu da waƙoƙinsa, inda sukan tiƙi rawa sosai duk sanda aka kunna waƙarsa.
‘Yan siyasa da ‘yan wasan cricket da ‘yan fim na Bollywood sun yi ta’aziyyar rasuwar, inda da yawa suka rinka tuna waƙoƙinsa da suka fi so.
Firaministan Indiya Narendra Modi, ya ce, ya kaɗu da rasuwar Lahiri.