Arsenal da Tottenham sun tashi 2-2 a wasan mako na shida a gasar Premier League karawar hamayya ta kungiyoyin Arewacin Landan ranar Lahadi.
Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Cristian Romero, wanda ya ci gida a minti na 26 da take leda a Emirates, amma sauran minti uku hutu Heung-min Son ya farke.
Daga baya ne Gunners ta kara na biyu ta hannun Bukayo Saka a bugun fenariti, bayan da Romero ya taÉ“a kwallo da hannu a da’ira ta 18.
Kenan Romaro ya zama É—an wasa na 11 a Premier League da ya ci gida ya kuma jawo bugun fenariti, kuma shi ne na farko a Tottenham.
Minti É—aya tsakani da Arsenal ta ci kwallo, Tottenham ta farke ta hannun Heung-min Son, hakan ya sa sun raba maki a tsakaninsu a wasan hamayya.
Har yanzu ba a doke Gunners ba da fara kakar bana a Premier har da wanda ta caskara PSV Eindhoven 4-0 a Champions League ranar Laraba.
Wasa na biyu kenan da Gunners ta raba maki a babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta fara yin 2-2 da Fulham a Emirates ranar 26 ga watan Agusta.
Ita ma dai Tottenham ba ta yi rashin nasara ba daga karawa shida da ta yi a Premier League ta kakar nan, wadda ta yi 2-2 a gidan Brentford ranar 13 ga watan Agusta