fidelitybank

Makashin Hanifa da ake zargi ya samu Lauya – Gwamnatin Kano

Date:

Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana cewa, Majalisar taimako ta sharia’a ta Najeriya ta bayyana bukata ta wakilci, Abdulmalik Tanko da sauran wadanda a ke zarginsu da kisan yarinya mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wannan ya biyo bayan umarnin mai shari’a, Usman Na’abba na babbar kotun jihar Kano ne a ranar 5 ga watan Fabrairu inda ya c,e jihar ta samarwa da Tanko da sauran mutum biyun lauya.

Lawan ya ce, duk wanda ke fuskantar shari’a kan zargin kisan kai, a na bukatar ya samu lauya, kuma idan mutum ba shi da lauya sannan ba shi da halin samowa, gwamnatin tarayya ta bukaci jiharsa da ta samar masa.

Ya yi bayanin cewa, Majalisar shari’ar ta Najeriya kafuwar gwamnatin tarayya ce wanda aikinsu ya kama da samar da lauya kyauta ga duk dan Najeriyan da bashi da lauya, kuma a ke zarginsa da kisan kai wanda hukuncinsa kai tsaye na kisa ne.

A na zargin Tanko da wasu mutum biyu da garkuwa tare da halaka Hanifa kuma shari’ar ta tsaya, saboda rashin lauyan wadanda ake zargin.

Bayan da alkali mai shari’a ya bayar da umarnin a samar musu da lauya, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp