Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar ta kai hari kan cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra’ila, wato Mossad.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda shalkwatar cibiyar Mossad ke ci da wuta.
Tasnim, ya ambato rundunar juyin juya halin Iran, na cewa ƙasar ta kai hari kan cibiyar ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami.
A wani saƙo da kamfanin dillancin labaran na Iran ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce: “A wani salo a ƙwarewa makaman IRGC masu linzami sun faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila, duk kuwa da ƙarfin tsaron sararin samaniya na zamani da ƙasar ke da shi.”
Kawo yanzu Isra’ila ba ta ce komai ba game da wannan iƙirari, kuma saboda dokokin taƙaita yaɗa labarai da gwamnati ta sanya, kafofofin yaɗa labaran da ke aiki a ƙasar ba za su iya bayar da labaran wasu wuraren da aka kai wa hari ba.