fidelitybank

Makamashi mai linzami kirar Rasha ya sauka a Poland

Date:

Gwamnatin Poland ta yi kira ga al’ummarta da su kwantar da hankalinsu,  bayan  da mutum biyu suka rasa rayukansu sanadin  fadawar wani makami mai linzami a wani kauye da ke kusa da kan iyakar kasar da Ukraine.

Shugaba Andrzej Duda ya ce makami ne da aka kera a Rasha amma babu cikakken bayani a kan wanda ya harba shi.

Shugaba Duda ya fada wa ‘yan jarida cewa : ”Ba mu da wata kwakkwarar shaida ya zuwa yanzu a kan wanda ya harbo makamin….akwai yuwar cewa makami ne  da aka kera a Rasha amma wani abu ne da ake gudanar da bincike a kansa a halin yanzu.”

Firaministan Poland Mateusz Morawiecki  ya ce gwamnati za ta tsaurara tsaro a sararin samaniyar kasar  sakamakon al’amarin da ya faru.

“ Mun yanke shawarar ganin cewa wasu daga cikin zababbun rundunoninmu na dakarun kasar  sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana musamman a fannin da ya shafi sa ido a kan  sararin samaniya” a jawabin da ya yi wa ‘yan jarida.

Al’amarin wanda ya janyo damuwa tsakanin mambobin kungiyar tsaro ta Nato wanda Poland mamba ce a ciki ya janyo musayar kalamai tsakanin Kyiv da kuma Moscow.

Rasha ta bayyana ikirarin da ake yi a kan cewa ita ce ta ke da alhaki a matsayin takalar fada daga wurin Kyiv wadda manufarta ita ce ta ja sauran kasashen duniya a cikin rikici  dan a yi mata taron-dangi

Sai dai a daya bangaren Ukraine ta yi watsi da zargin na Rasha, a kan cewa ita ce take da alhakin harin a matsayin ba komai ba ne illa kutungwila ce kawai daga Rasha.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba a shafinsa na Twitter ya ce: ”A yanzu Rasha ta gabatar da wani bayani da ya yi zargin cewa makamin  tsaron sararin samaniyar Ukraine ne ya fada a yankin Poland. Wannan kuma ba dai dai ba ne.”

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...
X whatsapp