Mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Ukraine shawara, Anton Herashchenko, ya ce, wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Belarus, ya faɗa kan wani filin jirgin sama a birnin Zhytomyr.
“Wannan ne abin da makamai suka hara daga Belarus da misalin ƙarfe 5:00 na yamma…mahara daga Belarus da Rasha sun hari filin jirgi na Zhytomyr,” a cewar Anton Herashchenko cikin wani saƙo a Telegram.
Wakilan Rasha da na Ukraine za su haɗu a kan iyakar Belarus da Ukraine, kamar yadda ofishin shugaban Ukraine ɗin ya faɗa ɗazu ba tare da bayyana yaushe ba.