Ministan tsaron Japan ya ce, wasu makamai masu linzami biyar na kasar China da aka harba a wani bangare na atisayen soji a kusa da Taiwan sun fada cikin ruwan wani yankin tattalin arzikinta.
Nubuo Kishi ya ce, wannan shi ne karo na farko da makamai masu linzami na kasar Sin za su fada cikin yankinta, inda Japan ta ce tana da hakkin gudanar da wasu ayyuka kamar kamun kifi da kuma hakowa.
Chinar ta harba makaman roka da makamai masu linzami a cikin ruwan da ke kewayen Taiwan, a yayin atisayen soji da ba a taɓa ganin irinsa ba, a matsayin martani ga ziyarar da ‘yar siyasar Amurka Nancy Pelosi ta kai wa yankin. In ji BBC.


