fidelitybank

Makaho da Kuturu sun shiga hannun NDLEA

Date:

Wani makaho mai shekaru 67, Aliyu Adebiyi da kuma wani kuturu, Haruna Abdullahi suna hannun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari, NDLEA, Mista Femi Babafemi, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, “An kama Adebiyi da 234kg na tabar wiwi.”

A cewar sanarwar, a jihar Osun, jami’an NDLEA a ranar Juma’a sun kama wani kaka makaho mai shekaru 67 mai suna Aliyu Adebiyi, wanda a gidansa suka gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 234 a kauyen Sokoto, Owena Ijesa, a karamar hukumar Atakumosa ta Gabas.

Kakakin ya bayyana cewa wani dillalin miyagun kwayoyi ya ajiye masa kayan a kan kudi Naira 6,000 duk wata kuma ya biya na tsawon watanni uku a gaba.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata a garin Garko da ke Kano, an kama Abdullahi mai shekaru 45, wanda ya yi kaurin suna wajen safarar muggan kwayoyi da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 2.2, inda ta kara da cewa an kwato nau’ukan diazepam da exol daban-daban daga gare shi.

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan Æ´ansanda mai kula da sashen kai É—auki na...

INEC za ta bai wa É—aurarru damar kaÉ—a Æ™uri’a a lokacin zaÉ“uka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

ÆŠaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon É—an takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaÉ—i mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaÉ—i...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp