Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), ta yi tir da harin ranar 24 ga watan Janairu da sojojin Najeriya suka kai kan wasu Fulani makiyaya a Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.
Harin ya yi sanadiyyar kashe mutum aƙalla 40, a cewar MDD.
Mai bai wa MDD shawara ta musamman kan kare kisan ƙare-dangi, Alice Nderitu, ita ce ta yi wadai da kisan, tana mai bayyana damuwa game da ƙaruwar hare-hare a arewa maso yamma da kuma tsakiyar kasa.
Karanta Wannan: MDD da ECOWAS ta gargadi Najeriya a kan zaben 2023
“Irin wannan hare-hare a kan mutane kawai saboda ƙabilarsu ka iya ta’azzara rikicin ƙabilanci, da shiga ƙungiyoyin ‘yan bindiga, da hare-haren ramuwar gayya, wanda zai dinga ƙarewa a kan fararen hula,” in ji ta.