Afirka ta Kudu ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aika da “dakarun kariya cikin gaggawa” don kare fararen hula daga hare-haren bama-bamai a yaƙin Isra’ila da Gaza.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar hulda da kasashen duniya ta bayyana damuwarta a cikin wata sanarwa kan yawan yaran da aka kashe a rikicin tare da zargin Isra’ila da keta dokokin ƙasashen duniya.
A daya bangaren kuma Isra’ila ta kare matakin da ta dauka na kai hare-hare a Gaza a matsayin kariyar kai biyo bayan kashe mutane 1,400 da Hamas ta yi a ranar 7 ga Oktoba yayin da kuma aka yi garkuwa da mutane 230.
Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutane 8,000 ne aka kashe tun bayan fara harin ramuwar gayya na Isra’ila.