Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da sauran ministocinsa sun yi tsit na minti daya domin nuna juyayi kan harin da ‘yan bindiga suka kai a jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.
Sun yi tsit din ne yayin zaman Majalisar Ministoci a Fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban binrin kasar.
Sun yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.
Harin dai ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas yayin da fiye da mutum 20 suka jikkata kuma suke jinya a wasu asibitoci da ke Kaduna.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kai harin kana ya bukaci jami’an tsaro su karfafa ayyukansu na kare rayukan ‘yan kasar.