fidelitybank

Majalisar Wakilan Najeriya ta mayar wa da Kamfanin Binance na Kirifto martani

Date:

Majalisar Wakilan Najeriya ta ce iƙirarin cin hanci da jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan ya ce wasu jami’ai a ƙasar sun buƙata daga gare shi – ba komai ba ne illa ɓata wa hukumomin ƙasar suna.

Mista Gambaryan, ya yi zargin cewa wasu ƴan majalisar wakilan ƙasar sun nemi ya ba su cin hancin dala miliyan 150 a lokacin da aka samu wata kiki-kaka tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Binance, lamarin da ya sa hukumomin Najeriya suka tsare Mista Gambaryan.

Cikin wata sanarwar da majalisar wakilan ta fitar, ta hannun mai magana da yawunta, Hon. Akin Rotimi,ta ce ”an yi zarge-zargen – waɗanda a shekarar da ta gabata ma an yi ta yawo da su – an yi ne domin ɓata wa wasu ƴan majalisar suna ba wai majalisar gaba ɗaya ba”.

“Majalisa na kira ga ƴan ƙasa su yi watsi da zarge-zargen marasa tabbas da aka ƙirƙira da nufin ɓata wa hukomomi da wasu jami’an ƙasar suna”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Majalisar ta kuma wanke ƴanmajalisaun da Mista Gambaryan ya ambata cikin zarge-zargen nasa.

“Ƴan majalisunj da aka ambata cikin zargin, sun tabbatar da jagorancin majalisa cewa babu wani abu makamancin zargin da ya auku tsakaninsu da mista Gambaryan, kamar yadda ya yi zargin”.

Kan haka ne sanarwar ta ce, ƴan majalisun za su ɗauki matakin shari’a kan Mista Gambaryan.

”Ɗaya daga ciki ma tuni ya shigar da ƙara kotu domin wanke kansa, yayin da aka ƙarfafa wa sauran biyun gwiwa su ma su yi hakan,” in ji sanarwar.

A kwanakin baya ne aka gurfanar da Gambaryan- ɗan Amurka a kotun Najeriya bisa zargin laifukan kuɗi.

To sai dai hukumomin Najeriya sun sake shi ne bayan shiga tsakani da gwamnatin Amurka ta yi.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a baya-bayan nan, Gambaryan ya yi ikirarin cewa kama shi da gwamnatin Najeriya ta yi ba bisa ƙa’ida ba ya sa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya kauce wa ganawar da ya shirya yi da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 (UNGA).

Ya kuma zargi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu kan lamarin, sannan ya ce gwamnatin Amurka ta rage yawan wakilan Najeriya da suka halarci taron na MDD.

Tuni dai gwamnatin Tinubu ta mayar masa ta martani kan zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe balle makama, tana mai bayyana su da tsantar ƙarya da ya shirya kuma da gangan.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp