fidelitybank

Majalisar wakilai za ta ɗaukaka ƙara a kan goge sashi na 84 a dokar Zaɓe

Date:

Majalisar Wakilan ta ƙasa ta yanke shawarar ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na bai wa Ministan Shari’a Abubakar Malami umarnin goge sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.

Majalisar ta nemi ministan shari’ar kuma antoni janar da ya dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala ɗaukaka ƙarar.

Ita ma Majalisar Dattawa ta ce, za ta ɗaukaka ƙarar bayan sanatoci da dama sun bijiro da buƙatar yin hakan a zamansu na yau Laraba.

Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya koka kan dalilin da ya sa aka kai ƙarar kotun da ke Jihar Abiya a Kudancin Najeriya, ya na mai cewa “majalisa ce kaɗai ke da ikon sauyawa ko yin doka a kundin tsarin mulkin Najeriya”.

Wakilin BBC da ya halarci zaman a Majalisar Dattawa ya ce, an samu ‘yar hatsaniya a lokacin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya buƙaci a cire sunansa daga jerin waɗanda suka amince a ɗaukaka ƙarar.

Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Neja ta Tsakiya na cikin ‘yan takarar neman shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya a zaɓen da a gudanar ranar 26 ga watan Maris.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp