fidelitybank

Majalisar Wakilai ta yi barazanar kama Emefiele

Date:

Shugaban Majalisar Wakilai ya yi barazanar bayar da umarnin a kamo Gwamnan Babban Bankin kasa, Godwin Emefiele da ya gurfana a gaban kwamitin da ke binciken cire tsoffin kudaden Naira.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan shugaban masu rinjaye na majalisar, Ado Doguwa ya sanar da shi cewa Emefiele da wasu sun ki gayyatar taron da aka yi ranar Laraba.

Da yake mayar da martani ga sanarwar, Gbajabiamila ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba ya umarci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Akali Baba da ya bayar da sammacin kama Emefiele da ya gurfana gaban kwamitin.

Mista Gbajabiamila ya kara da cewa ya kamata majalisar ta dage zamanta a yau domin shirin gudanar da zabe, amma za su tsaya tsayin daka domin warware rikicin musayar kudade.

“Ni bisa ga ikon da sashe na 89 (1) (d) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da tsari na 19 (2) (1) na Dokokin Majalisar Wakilai ya bayar, ba zan yi jinkirin bayar ba. takardar sammaci ga Sufeto Janar na Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ya tilasta wa babban bankin CBN ko manajan daraktocin da suka kasa amsa sammacin da Majalisar Wakilai ta yi, ko kuma suka yi sakaci.” Inji shi.

Ya kuma bayyana cewa wa’adin Emefiele bai yi daidai da sashe na 20 na dokar CBN ba, inda ya ce bankunan na tilastawa karbar tsofaffin takardun ko da wa’adin ya kare.

Idan dai ba a manta ba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda ake kyautata zaton shi ne Ubangidan Gbajabiamila, shi ma ya yi magana a kan manufar a ranar Alhamis yayin wani gangami.

Tinubu ya yi zargin cewa manufar ta shafi burinsa na shugaban kasa ne.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp