Majalisar Wakilai ta kasa ta kafa wani kwamatin bincike kan halin da gidajen yarin ƙasar ke ciki bayan wani rahoton BBC da ta fitar.
A ranar Litinin ne BBC ta yaɗa wani rahoto, bayan ta ziyarci wasu gidajen yari da tsofaffin fursunoni a yankin kudancin ƙasar nan.
Yayin zamanta na yau Laraba, majalisar ta bai wa kwamatin ta kan gyaran hukumomi damar ƙaddamar da bincike, sannan ya miƙa rahotonsa cikin mako takwas masu zuwa.
Akwai fursunoni kusan 70,000 a gidajen yarin kasar, kuma kimanin kashi 75 cikin 100 suna zaman jiran shari’a ne, a cewar hukumomi, yayin da cunkoso ya yi yawa matuƙa.
“Watannin farko da na shiga (gidan yari) na sha wahala. Mutane na mutuwa a kullum, kuma idan aka yi mutuwa cikin dare ba za su taɓa buɗe ƙofa ba har sai gari ya waye,” in ji Patrick wanda aka tsare shi shekara shida ba tare da shari’a ba.
Ya ƙara da cewa “ma’aikatan kurkukun mugaye ne, ba su da imani”.