Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed, domin gabatar da duk wasu takardu da suka shafi batun cire tallafin man fetur daga shekarar 2013 zuwa yau.
Dan majalisar wakilai Ibrahim Aliyu, shugaban kwamitin wucin gadi na musamman da ke binciken tsarin tallafin man fetur, ya bayyana haka a lokacin da Mista Stephen Okon, Daraktan kudi na cikin gida a ma’aikatar, ya bayyana a gaban sa a Abuja ranar Talata.
Shugaban kwamitin ya baiwa ministar a ranar 16 ga watan Agusta ta ba da kanta da duk wasu takardun da suka dace a cikin ikirarin tallafin.
Ya ce dole ne ministar ta amsa jimlar adadin da aka fitar daga asusun ajiyar kudaden shiga a matsayin biyan tallafin daga shekarar 2013 zuwa yau.