Shugaban Majalisar Turai, Charles Michel, ya yi maraba da sakamakon zaɓen kuma ya taya Macron murnar lashe shi bisa hasashen da aka yi.
Cikin wani saƙon Twitter, Mista Michael ya ce, ƙungiyarsu ta EU na buƙatar Faransa wadda za ta mayar da hankali manufar ƙungiyar da kuma Turai baki ɗaya.
Ita ma Shugabar Hukumar Turai, Usula von der Leyen, ta yi maraba sannan ta ce, tana jiran ci gaba da aiki da shugaban da aka sake zaɓa.