A ranar Talata ne majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ciyo bashin kuɗi daga ƙasashen waje da ya kai sama da dala biliyan 21 domin kashewa tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan bashi daga cikin gida da waje, wanda shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko, ya gabatar.
Akwai kuma shirin tara dala biliyan 2 daga cikin gida.
Tinubu ya ce za ayi amfani da bashin kuɗaɗen ne kan ɓangarorin gine-gine da noma da tsaro da wutar lantarki da fasahar sadarwa.
An ware dala biliyan 3 don farfaɗo da layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan shirin, inda suka ce hakan yana nuna adalci ga kowane yanki na ƙasar, kuma yana cikin tsarin da duniya ke bi wajen ci gaban tattalin arziki.