‘Yan majalisar dokokin jihar Oyo, sun dakatar da shugaban karamar hukumar Irepo, Hon. Sulaimon Lateef Adeniran.
‘Yan majalisar sun dauki matakin ne a zamansu na yau Talata.
Kakakin majalisar, Adebo Ogundoyin ya ce, ‘yan majalisar sun baiwa mataimakin shugaban majalisar, Hon. Joel ya dauki nauyin ayyukan gudanarwa na majalisa.
Mataimakin shugaban zai yi aiki ne har sai sakamakon kwamitin da aka kafa domin binciken zargin da ake yi wa shugaban karamar hukumar.