Majalisar dokokin jihar Sokoto, ta amince da buƙatar gwamna Ahmed Aliyu na kafa rundunar tsaron al’umma.
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan amincewa da wani rahoton haɗin gwiwa na kwamatocin majalisar kan tsaro da ayyuka na musamman da shari’a da haƙƙin jama’a.
Shugaban kwamitin, Alhaji Nasiru Adamu ya ba da rahoton cewa an yi nazari sosai kan ƙudirin inda aka samu shawarwari 28.
“Waɗan nan shawarwari sun haɗa da sauya sunan ƙudirin zuwa ƙudirin neman kafa rundunar samar da tsaron al’umma ta jihar Sokoto domin samar da zaman lafiya da tsaron rayuka da kuma dukiyoyin al’umma tare da kai ɗauki a lokutan gaggawa,” in ji shi.
Kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Tukur Bala ya gabatar da rahoton domin amincewa inda kuma ƴan majalisar suka amince da buƙatar ta hanyar kaɗa ƙuri’a.


