fidelitybank

Majalisar dokokin Osun za ta fara bincike akan bashin biliyan 407.32

Date:

Majalisar dokokin jihar Osun, ta sanar da shirin fara bincike kan bashin Naira biliyan 407.32 na jihar da gwamna Ademola Adeleke ya bayyana tun farko.

Nation ta tuna cewa Adeleke yayin da yake ganawa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Osun a ranar Alhamis ya bayyana cewa bashin Naira biliyan 407.32 ya ciyo magabacinsa, Adegboyega Oyetola yayin da ya sha alwashin yi masa tambayoyi kan bashin.

Sai dai Oyetola ya karyata maganar ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Ismail Omipidan cewa bai taba karbar wani lamuni ba tsawon shekara hudu amma gwamnatin Rauf Aregbesola ta ciwo bashin. Ya kalubalanci Adeleke da ya buga ranar da aka samu lamunin.

Hakazalika, Majalisar ta bakin Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Watsa Labarai na Majalisar, Kunle Akande a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta nuna damuwarta kan bayyana bashin tare da bayyana cewa an fara bincike kan rancen da jihar ta samu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Majalisar dokokin jihar Osun ta bayyana damuwarta kan yadda gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke ya bayyana bayyana bashi a jiya.

“Majalisa a matsayin wakilan jama’a da aka amince da su ya zama wajibi ta nemi karin haske tare da sanar da jama’ar jihar yadda ya kamata.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp