Majalisar dokokin jihar Kebbi a zamanta na zartaswar ranar Alhamis, ta bayyana kujerun tsohon kakakinta, Samaila Abdulmumini Kamba, da wasu ‘yan majalisar guda uku a matsayin ba kowa a wajen, saboda sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Sauran mambobin da abin ya shafa sun hada da Muhammad Buhari Aliero, Samaila Salihu Bui da Habibu Labbo Gwandu.
Aminiya ta tuna cewa an tsige Kamba ne a matsayin shugaban majalisar a shekarar da ta gabata bisa zarginsa da biyayya ga kungiyar Sanata Adamu Aliero. Bui bayan ya fice daga jam’iyyar APC an zabe shi mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar.
Magatakardar majalisar, Usman Ahmed Bunza, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin bayyana kujerun a matsayin “ya yi daidai da sashe na 109 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999.”