Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi Alhaji Kabiru Dashi (APC-Kiru) a matsayin mataimakin kakakin majalisar bayan, murabus din Malam Zubairu Massu wanda ya koma New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Zaben Dashi ya samo asali ne daga zaben da Mista Sale Marke (APC-Dawakin-Tofa) ya gabatar a zauren majalisar a jiya.
Nuhu Achika (APC-Wudil) ne ya goyi bayan nadin, bayan yan majalisar sun tabbatar da zabensa a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.