‘Yan majalisar dokokin jihar Kogi sun nesanta kansu daga sa hannun da aka tattara na tsige kakakin majalisar, Rt Hon. Mathew Kolawole.
‘Yan majalisar, wadanda suka bayyana hakan a ranar Talata yayin zaman majalisar, sun ce sun tattara sa hannun ne domin kada kuri’ar amincewa da kudirin Gwamna Yahaya Bello na shugaban kasa ba wai a tsige Shugaban Majalisar ba.
Matsayin ‘yan majalisar na zuwa ne kwanaki kadan bayan dakatarwar da tsohon mataimakin kakakin majalisar, Hon. Ahmed Mohammed mai wakiltar (Ankpa I) da wasu tsoffin manyan hafsoshi biyu, Hon. Bello Hassan Abdullahi (Ajaokuta), da Moses Odoo, (Dekina/Biraidu), sun shaida wa manema labarai cewa an tsige Yarima Mathew Kolawole a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi bisa zargin almundahana da kudi, babakere, cin zarafi na ofis, kin amincewa yi biyayya ga tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.
‘Yan majalisar, wadanda suka yi bi da bi suna magana a yayin zaman majalisar da Yarima Mathew Kolawole ya jagoranta sun tuna cewa a ranar 13 ga watan Mayun 2022, ‘yan majalisar sun amince da goyon bayan Gwamna Yahaya Bello na takarar shugaban kasa ba wai a tsige kakakin ba.
Da yake mayar da martani kan kalaman ‘yan majalisar, shugaban majalisar, Prince Mathew Kolawole, ya ce, ‘yan majalisar da aka dakatar sun saba wa dokar majalisar kuma kwamitin da’a da gata zai binciki su.