Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.
Majalisar ta amince da ƙudirin ne a yayin zaman ta na wannan rana ta talata, inda Sabbin masarautun masu daraja ta biyu da za su yi aiki a ƙarƙashin masarautar Kano mai daraja ta ɗaya.
Kuma dai Masarautun da Majalisar ta samar sun haɗar da:
1. Masarautar Rano: da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano- Bunkure da Kibiya.
2. Masarautar Ƙaraye: da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo
3. Masarautar Gaya: da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya- Ajingi da Albasu.


