Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana kujerun ‘yan majalisar wakilai 3 da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP ba kowa.
Hakan ya biyo bayan wasikar murabus din da aka ce ‘yan majalisar uku da suka yi murabus daga kujerunsu ne suka rubuta.
Kakakin majalisar Francis Nwifuru ne ya karanta wasikar a zaman gaggawar da majalisar ta yi a ranar Talata.
‘Yan majalisar uku su ne Ali Okechukwu mai wakiltar Ishielu ta Arewa; da Franca Okpo mai wakiltar Abakaliki ta Arewa da kuma Victor Aleke mai wakiltar Ebonyi ta Yamma.