fidelitybank

Majalisar dokoki na son Iran ta yanke hulɗa da hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya

Date:

Majalisar dokokin Iran ta kaɗa ƙuri’a domin yanke hulɗa da hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IAEA), in ji rahotanni daga kafafen yaɗa labaran gwamnati.

Shugaban majalisar, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce hukumar IAEA ta gaza yin Allah-wadai da hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan wuraren nukiliyar Iran, lamarin da ya sa majalisar dokokin Iran ɗin ta yanke wannan shawarar.

Ghalibaf ya ce hukumomin nukiliya na Iran za su “dakatar da haɗin kai da IAEA har sai an tabbatar da tsaron wuraren da ake sarrafa makamashin nukiliya”.

Ya kuma ƙara da cewa shirin Iran na nukiliya “zai ci gaba da tafiya cikin sauri da aminci”.

Amma kuma wannan ƙuri’ar da aka kaɗa, sai an samu amincewa daga manyan jagororin gwamnati kafin ta zama doka a hukumance.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp