Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana cewa daga ƙarshen watan Yuli, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga mutum miliyan 1.3 a arewa maso gabashin Najeriya saboda ƙarancin kuɗi.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa, kuma yunwa na kai matsayi mafi muni a tarihin ƙasar.
WFP ya ce kayan abinci da na kiwon lafiya sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake yi yanzu shi ne na ƙarshe.
Idan ba a samu tallafi cikin gaggawa ba, mutane da dama za su fuskanci yunwa, gudun hijira ko kuma shiga hannun ‘yan tada ƙayar baya.
Daraktan WFP a Najeriya, David Stevenson, ya ce kusan mutum miliyan 31 ke fama da matsanancin yunwa a ƙasar wanda shine mafi yawa a tarihi.
“Yara ƙanana za su fi shan wahala, domin fiye da asibitoci 150 a Borno da Yobe da ke kula da yara ƙasa da shekaru biyu za su rufe.” in ji daraktan.
WFP na buƙatar dala miliyan 130 domin cigaba da ayyukanta har zuwa ƙarshen shekarar 2025.