Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace ‘yan gudun hijira masu yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotonni sun ce akallah ‘yan gudun hijira 200 ne galibinsu mata da ƙananan yara da ‘yan mata mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da su a ƙarshen mako, kodayake har yanzu a hukumance ba a tabbatar da aadin mutanen ba.
Mayaƙan sun saki wasu tsoffin mata da ƙananna yara ‘yan kasa da shekara 10.
Cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba, Majalisar Dinkin Duniyar ta bakin kodinetan ayyukan jin ƙai a Najeriya, Mohammed Malick Fall, ya ce sace mutanen masu yawa, ”tunatarwa ce cewa mata da ‘yan mata na daga cikin mutanen da ke ciki hatsarin harin mayaƙan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a makon da ya gabata a lokacin da ‘yan gudun hijirar suka tafi neman itacen girki.
yayin da yake jajanta wa iyalan ‘yan uwan waɗanda lamarin ya shafa, Mista Malik Fall ya buƙaci hukumomi su samar wa mazauna sansanonin gudun hijira sana’o’i da ayyukan yi don rage hatsarin da suke ciki.
Aƙalla mutum 40,000 ne aka kashe tare da raba fiye da miliyan biyu da muhallansu cikin fiye da shekara 10 na yakin Boko Haram.
Mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira na fama da ƙarancin abinci, Inda ake kashe su ko sace su tare da tilasta musu shiga ƙungiyoyin masu dauke da makamai idan suka yi yunƙurin zuwa gonakinsu ko neman abinci.
Haka kuma a wasu lokuta mayaƙan kan ci zarafinsu, inda suke tilasta musu auren mayaƙan.