Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna damuwa kan tsaron lafiyar hamɓararren shugaban Nijar Muhammad Bazoum da na iyalansa, wanda ya ce ana tsare da shi cikin yanayi mara kyau.
Nan gaba a yau ake sa ran shugabannin ƙassahen Ecowas za su gana a Abuja babban birnin Najeriya kan batun ƙasar ta Nijar.
A ranar Laraba ma Amurka ta bayyana irin wannan damuwa kan halin da Bazoum ɗin yake ciki.