Har yanzu dai game da wasiƙar da Babban Sakataren MDD António Guterres ya rubuta, inda ya nemi a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas a Zirin Gaza.
Ya yi amfani da ayar doka ta 99 ta MDD, wadda ta ba shi damar jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan “duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro”.
“Yayin da ake fuskantar shiga bala’in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala’i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji,” in ji shi ciki wani saƙo da ya walafa a dandalin X.
Ya ce wannan ne karon farko da ya yi hakan tun da ya zama sakatare janar a 2017.
Cikin wasiƙar da ya rubuta wa shugaban Kwamatin Tsaron, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin