Majalisar dattijai ta amince da kudirin doka mai lamba 58 da ke neman bai wa ‘yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takara.
The Nation ta rawaito cewa, majalisar ta yi watsi da wani kudirin doka da ke neman bai wa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje damar kada kuri’a a lokacin zabe.
A gefe guda kuma, ‘yan majalisar sun ki amincewa da wani kudirin doka da ke neman samar da zaben Magajin Gari a Babban Birnin Tarayya, an samu kuri’u 62 da suka amince da hakan. A ka’ida a na bukatar kuri’u 73, domin amincewa da kudirin.
Har ila yau, wani kudirin doka da ke neman tabbatar da cewa mutumin da ya yi rajistar zabe kuma mazaunin FCT ne zai zama Minista mai wakiltar FCT shi ma ya sha kasa a majalisar.