Majalisar dokokin kasar za ta yi wa dokar zabe na 2022 kwaskwarima, domin kare rauni a cikin dokar.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, a ranar Talata yayin zaman majalisar, ya bayyana hakan, biyo bayan wani muhimmin batu da Sanata Yahaya Abdullahi (APC, Kebbi ta Arewa) ya gabatar a zauren majalisar.
Yayin da yake bayyana hukuncin kotun koli kan sashe na 84 (12) na dokar zabe a matsayin wani hukunci mai cike da tarihi da ya tabbatar da majalisar dokokin kasar, Sanata Lawan ya bayyana cewa kara yin kwaskwarima ga dokar zai karfafa ta gabanin babban zaben 2023.
Ya ce, “Bari in ce wannan wani muhimmin hukunci ne da kotun koli ta yanke, cewa majalisar dokokin kasar sun yi aikinsu kuma kotu ta tabbatar da hakan.
“Tunanin irin hanyar da ya kamata a bi na zaben fidda gwani a halin yanzu an bar jam’iyyun siyasa su yanke shawara.
“Amma yayin da muke aiwatar da dokar zabe ta 2022, ya kamata mu lura da karfi da raunin dokar. Ya kamata wannan doka ta inganta tsarin zabe da tsarin zabe a kasarmu.