Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce, a ranar 29 ga watan Yuni ne majalisar dattawa za ta tantance mutane bakwai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya miƙa sunan su domin nada su a matsayin ministoci.
Lawan ya sanar da hakan ne a jiya a gaban majalisar dattawa wadda ta dage zaman majalisar har sai ranar 28 ga watan Yuni.
“Za a tantance wadanda aka nada a matsayin ministoci ranar Laraba mako mai zuwa,” in ji shi
Shugaba Buhari, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da tantance sunayen ministoci bakwai.
Wadanda aka nada don tabbatarwa sun hada da: Henry Ikechukwu Ikoh (Abia), Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Ekumamankama Joseph Nkama (Ebonyi) da Goodluck Nanah Opiah (Imo).
Sauran sun hada da: Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) Ademola Adewole Adegoroye (Ondo) da Odum Udi (Rivers).