fidelitybank

Majalisar Dattawa za ta samar da dokokin rage illar bala’o’i – Sanatocin Arewa

Date:

Majalisar dattawa na shirin samar da wasu dokoki da nufin rage illar bala’o’in muhalli kamar su ambaliyar ruwa a ƙasar.

Hakan ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta yi ɓarna a Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Talata bayan rushewar madatsar ruwa ta Alau.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban Sanatoci na yakin Arewa, Abdulaziz Musa Yar’adua ya fitar ranar Alhamis a Abuja kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya ce, “Majalisar Dattawa za ta ci gaba da aiwatar da dokoki da tsare-tsare da za su daƙile illolin bala’o’in muhalli da kuma samar da ci gaba mai dorewa.”

“Muna goyon bayan al’ummar jihar Borno tare da tabbatar musu da goyon bayanmu a wannan mawuyacin lokaci.”

Sanarwar ta buƙaci gwamnatocin jihohi 36 na tarayyar ƙasar da su tsara manyan tsare-tsare don tunkarar matsalar sauyin yanayi a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile bala’o’in muhalli kamar su ambaliyar ruwa.

Sanarwar ta kuma yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da Naira biliyan 3 a matsayin asusun shiga tsakani ga wadanda bala’in ya rutsa da su tare da jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Borno dangane da ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da lalata gidaje da gonaki.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp