Majalisar dattawa ta amince da kudurin dokar kafa karin makarantun koyon aikin lauya a bangarorin shida na fadin kasar nan.
Majalisar ta amince da kudurin a zaman da ta yi yau Talata, 08 ga watan Fabrairu na 2022, bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan harkokin shari’a da hakkin dan Adam.
Jaridar DailyTrust ta rawaito, makarantun da ake da su a yanzu su ne wadda take a Abuja; yankin Arewa ta tsakiya, sai ta Kano, wadda ke Bagauda yankin Arewa maso Yamma, sai ta Yola yankin Arewa maso Gabas, sai ta jihar Legas, yankin Kudu maso Yamma da ta Enugu yankin Kudu maso Gabas, da kuma ta Yenegoa a yankin Kudu maso Kudu.
Wadanda aka amince a kara sun hada da wadda za a yi a Kabba jihar Kogi a Arewa ta tsakiya da wata a Jos a yankin Arewa maso tsakiyar ita ma,
da ta Maiduguri a jihar Borno domin Arewa maso Gabas, sai ta Argungu a jihar Kebbi yankin Arewa maso Yamma.
Sauran su ne ta Okija a jihar Anambra a yankin Kudu maso Gabas sai ta
Orogun a jihar Delta yankin kudu maso kudu, sai kuma ta Ilawe da ke jihar Ekiti a Kudu maso Yamma.