Majalisar dokoki ta fara shirye-shiryen yi wa sababbin zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattawan majalisa ta 10 bitar ayyukan majalisar.
Bitar za ta taimaka wajen ilimantar da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wajen sanin makamai aikin majalisar.
Cibiyar kula da ayyukan majalisa da dimokradiyya, ta ce, bitar na da matuƙar muhimmanci kasancewar fiye da kashi 70 cikin 100, na zaɓaɓɓun ‘yan majalisar, karon su na farko kenan da suke zuwa majalisar.
A cikin watan Yuni mai zuwa ne za a rantsar da majalisar wadda ita ce ta 10.