fidelitybank

Majalisa za ta binciki yadda wutar Najeriya ke lalacewa

Date:

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta da ke kula da harkokin wutar lantarki ya gudanar da bincike kan matsalar yawan lalacewar layin samar da lantarki na ƙasar, ya kuma bayar da rahoto cikin mako uku.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, matakin ya biyo bayan amincewa da buƙatar da ɗan majalisar Mansur Mano Soro, daga jihar Bauchi ya gabatar a zamanta na yau Laraba.

Ɗan majalisar ya bayyana damuwa kan matsalar lalacewar layin lantarkin na ƙasa da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a kwanakin nan, lamarin da ke jefa ƙasar cikin rashin wuta tare da jefa ‘yan ƙasar cikin matsin rayuwa da suke fama da shi.

Ya ce, wutar lantarki aba ce da ta zama wajibi wajen bunƙasar tattalin arziƙi da kuma cigaban duk wata ƙasa.

Hon. Mansur ya nuna takaicinsa yadda aka samu matsalar lalacewar layin wutar na ƙasa sau takwas a cikin wannan shekara ta 2024 kaɗai, inda ya bayyana hakan a matsayin abin damuwa da takaici.

Ɗan majalisar ya ce sakamakon matsalar lalacewar, gaba ɗaya yankin arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas na ƙasar sun kasance cikin duhu, da uwa uba ƙarin tsanani na tsadar rayuwa.

Ya ƙara da cewa abin takaici ne yadda matsalar ke faruwa a daidai lokacin da ministan wutar lantarkin ke ba wa ‘yan Najeriya tabbacin ingancin samar da wutar, abin da ya sa har gwamnati ta ce ya sa dole ta ƙara kuɗin wutar ga masu amfani da ita na rukunin farko ko babban layi (Band A ).

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp