Kwamitin tsaron ƙasa da bayanan sirri na majalisar wakilan Najeriya ya yanke shawarar kafa kwamitin ƙawararru don maganace matsalar da ke janyo yawan lalacewar jiragen sama na fadar shugaban kasar.
A jiya Litinin ne ƴan kwamitin suka yi wata ganawar sirri da kwamandan da ke kula da jiragen saman shugaban ƙasar, Air Vice Marshal Olayinka Olusola, a majalisar, a Abuja, domin tattaunawa a kan abin da ya kai ga Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka yi amfani da jiragen haya a kwanan nan.
A watan Afirilu ne Shugaban ya yi amfani da jirgin haya daga Netherlands zuwa Saudiyya domin halartar taron koli na duniya kan tattalin arziƙ.
Haka kuma mako biyu da ya gabata aka soke tafiyar da Mataimakin Shugaban Ƙasar Kashim Shettima zai yi inda zai wakilci Shugaba Tinubu a taron koli na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Afirka kan kasuwanci saboda matsalar da jirgin da zai hau ya gamu da ita.
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Ahmad Satomi ya ce a muhawarar da suka yi kan batun, ƴan majalisar sun yanke shawarar gayyatar mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro Nuhu Ribadu da kuma kwamandan da ke kula da jiragen fadar shugaban kasar da su je su yi bayani kan yawan lalacewar jiragen saman duk da maƙudan kuɗaɗen da ake ware musu a kasafin kuɗin duk shekara don kula da su.