Kwamitin majaisar wakilai kan kula da kadarorin gwamnati ya ce zai fara bincike game da wani batun sayar da jirgin helikwafta na kwalejin koyar da tuƙin jirgin sama ta Najeriya da ke Zaria.
Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaban kwamiin, Ademorin Kuye a cikin wata sanarwa yana cewa za su binciki yadda aka sayar da helikwaftan ƙirar Bell 206L-3 wanda aka sayo da dukiyar al’umma.
Ya ce gwamnati ta sayar da jirgin ne a daidai lokacin da rundunar sojin ruwa take buƙatar irinsa don inganta ayyukanta.
“Kwamitinmu zai binciki yadda aka sayar da wannan kadara ta gwamnati mai amfani sosai wajen horas da matuƙa jirgin sama, don tabbatar da cewa an bi ƙa’ida kuma ba a cuci ƙasarmu a cinikin ba” in ji Ademorin Kuye.
A ranar Alhamis da ta gabata ne, kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya ƙaddamar da kwamitocin majalisar, kafin sanar da tafiya hutu.