Majalisar dattawa ta yi gyara ga dokar ta’addanci, 2013, inda ta haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Ƙaddamar da Dokar Ta’addanci na 2013, ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar dattijai kan harkokin shari’a, ‘yancin ɗan adam da shari’a.
Shugaban kwamitin, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya) ne ya gabatar da rahoton kafin a duba.
Bamidele, a cikin jawabinsa, ya ce kudirin dokar ya tanadi haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda, domin a sako duk wani wanda aka tsare ba bisa ka’ida ba, daure ko kuma sace shi.
A cewar dan majalisar, “Babban abin da aka shigo da wannan kudiri shi ne don dakile karuwar satar mutane da sace-sacen kudin fansa a Najeriya, wanda ke yaduwa a fadin kasar.”
Ya bayyana cewa, a cikin takardar da aka gabatar wa kwamitin, an tabo batutuwan da suka shafi batun ta’addanci da kuma bayar da kudaden ta’addanci daidai da kyawawan ayyuka na duniya.