fidelitybank

Majalisa ta umarci Gwamnati ta dakatar da yarjejeniyar SAMOA da ta janyo cece-kuce a kan auren jinsi

Date:

Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta dakatar da yarjejeniyar Samoa da ta tayar da ƙura a kasar nan.

A zaman da ta yi yau Talata, majalisar ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai gwamnati ta fito ta bayyana ɓangarorin yarjejeniyar da suka haifar da cecekuce.

Ɗan majalisar wakilai Hon Aliyu Madaki wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin ya ce, majalisar ta kuma nemi ministocin da suka jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar su gurfana gabanta tare da takardun yarjejeniyar domin buƙatar fayyace komi musamman “ɓangaren da ke bayani kan daidaiton jinsi.”

Yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanya wa hannu da Tarayyar Turai ta tayar da ƙura a Najeriya, inda wasu da dama suka nuna fushinsu musamman zargin cewa yarjejeniyar na ƙunshe da wani ɓangare da ke nuna goyon baya da kuma kare muradun masu maɗigo da luwaɗi.

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta, inda ministan kasafin kudi da tsare-tsare da kuma ministan yaɗa labarai suka ce, Najeriya ba za ta taɓa amincewa da wata yarjejeniyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma al’adu da addini ba.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp